✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan sufurin jiragen kasa sun janye yajin aiki

An janye yajin aikin bayan Gwamnatin Tarayya ta amince ta biya bukatun ma'aikatan .

Ma’aikatan Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga.

A ranar Juma’a da dare muka samu labarin janye yajin aikin gargadin na kwana uku da ma’aikatan suka shiga.

Sun janye yajin aikin ne bayan zaman da Kwamitin Daraktocin Hukumatar da kuma Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ta yi ta su a Abuja.

“Da wannan sanarwa da sauran abubuwan da aka cimma matsaya a kai, an janye yajin aikin gargadin, ana kuma umartar dukkan ma’aikata su koma bakin aikinsu nan take,” inji sanarwar bayan taron.

Sanarwar ta ce taron ya kafa kwamitin masu ruwa da tsaki da zai yi nazari kan yanayin aikin ma’aikatan, ya muka mika rahotonsa zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2022.

Zaman ya kuma yi ittifakin cewa a tattara bayanan duk ma’aikatan hukumar da suka rasu domin a biya iyalansu hakkokinsu.

An kuma tattauna batun karin albashin, wanda Ma’aikatar Sufurin da Kwamitin Daraktocin Hukumar suka yi alkawarin gabatar wa Gwamantin Tarayya domin aiwatarwa nan ba da jima ba.

Idan ba a manta ba Aminiya ta kawo rahoto cewa a ranar Alhamis ma’aikatan suka fara yajin aiki domin neman karin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu.