✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki

Akwai yiwuwar Najeriya ta shiga matsalar wutar lantarki yayin da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) suka fara yajin aiki a ranar Laraba. Ma’aikatan sun…

Akwai yiwuwar Najeriya ta shiga matsalar wutar lantarki yayin da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) suka fara yajin aiki a ranar Laraba.

Ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin ne don nuna rashin amincewarsu ga wani shiri na ganawa ta dole da hukumar za ta yi wa wadanda ta ke so ta karawa girma, da kuma wasu batutuwan da suke damunsu.

’Yan kungiyar sun fara gudanar da yajin aikin ne a ranar Talata a inda suka rufe kofar shiga Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) da ke Abuja.

Kungiyar ta bayar da sanarwar soma yajin aikin ne tare da ikirarin za ta soma shi ka’in da na’in a ranar Laraba.

Babban Sakataren kungiyar na kasa, Joe Ajaero a wata sanarwa da ya sa wa hannu a ranar Litinin, ya ce suna adawa ne ga wani umarni da kamfanin na TCN ya bayar.

Umarnin ya tilasta wa duk wadanda ke kan mukamin Manaja da masu shirin zuwa mukamin Mataimakan Manaja da su je a gana da su wanda suka ce hakan ya saba wa tsarin aikin hukumar.

A cewarsa, wasu korafe-korafen ma’aikatar sun hada da tsangwama daga ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da a ke nuna wa ma’aikatan da suka fito daga bangaren samar da makamashi.

Minista a Ma’aikatar Lantarki, Goddy Jedy-Agba, ya rarrashi ma’aikatan yana mai kira a garesu da su zauna a teburin shawara.

Wata wasika da wani babban jami’in hukumar, Injiniya Yusuf Abdulaziz, ya aika wa kungiyar ma’aikatan ya ce an dakatar da ganawar har sai an tattauna da kungiyar ma’aikatan.