✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’auratan da suke sakin juna su sake aure duk shekara 3

Sun amince duk bayan shekara 3 su sake yin aure

Wadansu ma’aurata ’yan kasar Japan da ba su amince da yin amfani da sunan iyayensu ba, sun amince duk bayan shekara 3 su sake yin aure, bayan sun saki junansu don su yi amfani da wasu sunayen iyayen da suke bukata.

Dokar Japan ta bayyana cewa, dole ne ma’aurata su amince da suna daya tilo na iyaye da za su yi amfani da shi bayan sun yi aure, amma sai ga ma’auratan biyu sun kasa tsaida wane sunan iyayensu za su yi amfani da shi.

Wadannan ma’aurata biyu daga birnin Hachioji, da ke wajen birnin Tokyo, sun tsinci kansu a wani yanayi da suka yanke shawarar yin aure, bayan wasu ’yan watanni da yin alkawarin aure.

Sai da aka zo maganar sunan iyaye, ya bayyana cewa amaryar ta yi niyya ta boye sunanta, abin da mijinta bai
yarda da shi ba.

Sun dan yi jayayya na dan lokaci, amma
sai suka yanke shawarar cewa, ba su ne ma’aurata na farko da suka samu wannan matsalar ba, kuma akwai hanyar da za a iya magance ta.

“Mijina (wanda saurayinta ne a lokacin) ya yi tunanin cewa ya kamata mata su yi amfani da sunan mijinsu a matsayin sunan iyaye. Ban yarda da hakan ba, sai muka yi gardama,” matar wacce ma’aikaciya ce, ta bayyana wa jaridar Japan Mainichi kwanakin baya.

Mai jiran zama amaryar ta ji takaicin rashin iya rike sunanta na budurwa, har ta kai sai da saurayin nata ya kai korafi ga wadansu kawayenta.

A lokacin ne ya gano wadansu ma’aurata na fama da matsala iri daya da tasu, inda suka yi nasarar magance matsalar ta hanyar yin saki da sake wani auren lokaci zuwa lokaci kuma ta sauya sunan iyaye a tsakaninsu.

Wanda shi ne ainihin abin da suka yanke shawarar yi.

Bayan mutumin wanda ma’aikacin gwamnati ne ya gabatar da mafita ga budurwar, sai suka yanke shawarar yin
haka.

A cikin shekarar 2016, sun yi aure a karon farko kuma suna amfani da sunan iyayensa tsawon shekara uku.

Sannan, a shekarar 2019, suka rabu sannan suka sake yin aure, suna amfani da sunan iyayen matar.

A watan Yulin bara, sun shirya sake sake yin aurensu, bayan sun shirya za su sake yin aure ta hanyar amfani da sunan iyayen mijin.

Amma wannan sulhu ya warware saboda rashin jituwar ma’auratan, wadanda suka gwammace a sakaya sunansu, dukkansu sun yarda cewa, a lokacin canza sunan iyayensu lokaci zuwa lokaci akan dan samun matsala.

Har yanzu mijin yana amfani da sunan iyayensa a wurin aiki, amma idan ana batun tsari a takarda akan dan samun rudani.

“Koyaushe ina tuna wa kaina cewa, ina dauke da sunan iyayen matata ce,” inji shi.

Kodayake tsarin yana da wuyar gaske ga wadansu ma’aurata, sun ce shi ne kawai mafita a gare su.

Wata hanyar da suka sani ita ce, fita kasar waje su yi aure da sunayen iyayensu, kafin su koma gida su nemi kotun Japan ta amince da aurensu duk da sunansu daban-daban ne.

Da alama sun yi tunanin hanyar da suka dauka ta fi sauki.