✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mace 1 na mutuwa duk minti 2 wajen haihuwa —WHO

Rahoton ya ce an samu karuwar mace-macen mata masu juna biyu a wasu yankuna.

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar ya nuna akalla mace daya na mutuwa kusan kowane minti biyu a yayin haihuwa a shekarar 2020.

Rahoton, wanda aka fitar a ranar Alhamis, ya ce a 2020 “kimanin mata 287,000 ne a fadin duniya suka mutu ta dalilin haihuwa, kwatankwacin mata masu ciki 800 dak mutuwa a kowace rana, sannan mace daya a kowane minti biyu.”

Adadin ya karu idan aka kwatanta da kiyasin mutuwar mata masu juna biyu 446,000 cikin shekara 20 da suka gabata, a cewar rahoton.

Duk da haka, yayin da adadin mace-macen mata masu juna biyu lokacin haihuwa ya ragu a tsakanin 2000 zuwa 2015, amma ya karu a wasu yankuna.

A halin da ake ciki WHO, ta ce lamarin ya fi kamari a yankunan da ke fama da talauci da kuma kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula.

WHO ta ce an samu kashi 70 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu a duniya a 2020, sai kuma Tsakiya da Kudancin Asiya wanda aka samu kashi 17 cikin 100.

Catherine Russell, Babbar Daraktar Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), daya daga cikin kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da mace-macen mata masu juna biyu (MMEIG) ta ce bai kamata a ji tsoron haihuwa ba.

“Babu wata uwa da za ta ji tsoro don rayuwarta yayin da ta ke kokarin haifar jariri ba, musamman lokacin da ilimi da kayan aikin magance matsalolin haihuwa suka wadata.”

Abubuwan da za a iya kiyayewa wadanda ke haifar da mutuwar mata masu juna biyu sun hadar da zubar da jini mai yawa, hawan jini, zubar da ciki, cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) da zazzabin cizon sauro.

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce daga cikin mace-macen da aka samu za a iya shawo kansu

Daya daga cikin manufofin Majalisar Dinkin Duniya (SDGs) shi ne rage mace-macen mata masu juna biyu nan da 2030.

Rahoton ya ce kara daukar matakan kula da lafiyar mata masu juna na daga cikin abubuwan da za a bi domin cimma wannan manufa.