✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mace ta farko da aka zaba Firaminista a Sweden ta yi murabus sa’o’i bayan nada ta

Magdalena Andersson ta yi murabus sa'o'i bayan nadinta a matsayin Firaministan Sweden.

Mace ta farko a tarihi da aka zaba Firaminista a Kasar Sweden, Magdalena Andersson, ta yi murabus daga mukamin sa’o’i bayan nadin da Majalisar Dokokin Kasar ta yi mata.

A Larabar da ta gabata ce Firaminista Magdalena ta yi murabus bayan kasafin kudin kasar da ta gabatar ya gaza samun shiga sannan kuma da janyewar jam’iyyar ‘Green Party’ daga hadakar da suka yi.

Kafar Labarai ta CBS ta ruwaito cewa, an yi watsi da kasafin kudin da Magdalena ta gabatar sakamon samun shiga da wanda jami’yyar adawa ta gabatar ciki har da masu ra’ayin rikau na Sweden Democrats.

A jawabin da ta gabatar yayin zantawa da manema labarai, Magdalena ta ce ta yanke shawarar hakan ce saboda ta kare mutuncinta, inda ta bayyana cewa ba za ta so ta jagoranci gwamnatin da daga baya za a zo ana tababa a kan halaccinta.

Da take ci gaba da bayyana hujjar murabus dinta daga mukamin Firaminista bayan tsawon lokacin da bai wuce sa’o’i bakwai a kujerar ba, Magdalena ta ce tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa abu mafi dacewa shi ne duk wata gwamnatin hadaka ta yi murabus a duk lokacin da abokiyar hadakarta ta janye

Ta ce tana fata a sake zabenta nan ba da jimawa ba a matsayin shugabar gwamnati mara rinjaye da ta kunshi jam’iyyar Social Democrats ne kawai.

A cikin wani yanayi mai cike da rudani, Magdalena wacce ta zama mace ta farko da aka zaba kan mukamin firaminista a kasar Sweden bayan da ta kulla yarjejeniyar karshe da jam’iyyar mai sassaucin ra’ayi ta wajen kara kudaden fansho don samun goyon bayanta a zaben na ranar Laraba.

Amma sai daya jam’iyyar ta masu rajin kare muhalli ta janye goyon bayanta ga kasafin kudin da Magdalena ta gabatar, saboda yadda ta amince da kudirin masu sassaucin ra’ayi, lamarin da ya hana kasafin da ta gabatar samun shiga sakamakon karancin kuri’u.