Da yake sanar da hakan, Minista a Ma’aikatar, Dokta Olorunnimbe Adeleke Mamora, ya ce mutum 479 ne macizai suke sara a cikin kowadanne mutum 100,000 a Najeriya a duk shekara.

Babban Sakataren Ma’aikatar, Mahmoud Mamman, ya ce mutum 1,793 sun rasu a sakamakon sarar maciji daga 2018 zuwa 2020 inda macizai suka sari mutum 45,834, duk da cewa babu alkaluman wadansu mutanen da macizai suka sara ba.

“Shi ya sa muke kokarin hadin gwiwa da kawayenmu domin yin taron dangi mu shawo kan matsalar da kuma magance aukuwarta,”  a cewar Mamman.

A jawabinsa na Ranar Wayar da Kai game da Saran Macizai ta bana, Mamora ya ce jihohin da matsalar ta fi kamari a Najeriya su ne Gombe, Filato, Adamawa, Bauchi, Borno, Nasarawa, Enugu, Kogi, Kebbi, Oyo, Binuwai da kuma Taraba.

Mamora ya yi kira a kara kaimi da hadin gwiwa tsakanin jihohin da  matsalar ta fi kamari da kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin yi wa tufkar hanci.

Wani kwararre a fannin lafiya, Dokta Alex Okoh, ya ce kumanin mutumin miliyan daya ne macizai suke sara a duk shekara a Nahiyar Afirka, wadanda kusan rabinsu ke bukatar magani, kuma matsalar ta fi kamari ne a yankunan karkara.