✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid za ta dauko Haaland, Pogba da Mbappe a watan Janairu

Jaridar Football Insider ta ambato cewa Paul Pogba ya buga wasansa na karshe a Manchester United.

Akwai yiwuwar Erling Braut Haaland, dan wasan gaban Borussia Dortmund mai shekara 21 ya koma Barcelona idan kungiyar ta samu damar buga gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa. Sport

Sabon kocin Manchester United, Ralf Rangnick, ya shiga wawason neman dan bayan Chelsea, Antonio Rudiger mai shekara 28 wanda kungiyoyin Bayern Munich da Paris St. Germain ke zawarci. Bild

Kocin Roma, Jose Mourinho ya kyallara idanunsa kan dan wasan tsakiya na kungiyar Chelsea da Ingila, Ruben Loftus-Cheek mai shekara  25. Sun

Real Madrid na son ta yi zari wajen dauko Haaland da Kylian Mbappe na PSG idan an bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a watan Janairu. Fichajes

Jaridar Football Insider ta ambato cewa Paul Pogba ya buga wasansa na karshe a Manchester United, inda zai bar kungiyar a watan Janairu kuma dan wasan zai koma Real Madrid wanda ta jima tana zawarcinsa.

Barcelona ta yi wa Tottenham da Newcastle tallar dan wasanta na kasar Brazil, Philippe Coutinho. Goal

Chelsea ta soma zawarcin dan wasan bayan Wolves na Portugal, Ruben Neves. Todo Fichajes

Atletico Madrid na shirin barin dan wasan bayanta, Kieran Trippier ya tafi Newcastle kan fam miliyan 15 idan har sun samu wani dan wasan da zai maye gurbinsa. Mail

Manchester City na shirin tsawaita kwantaragin dan wasanta na tsakiya na kasar Portugal, Bernardo Silva a watan Janairu, inda za ta ninka masa albashinsa. Sun