✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar Turai

A yanzu Chelsea tana bukatar cin kwallaye biyu kacal ta sauya makomar wasan.

A daren ranar Talatar nan za a fafata tsakanin kungiyar Real Madrid da Chelsea a gasar Cin Kofin Zakarun Turai, inda ake saran kungiya daya daga cikinsu ta samu damar wucewa zuwa zagaye na gaba na semi final.

A karawar da aka yi makon jiya, Madrid ta doke Chelsea mai rike da kofin gasar da ci 3-1 a wasan da ya gudana a Ingila wanda Karim Benzema ya jefa kwallayen guda 3 shi kadai.

Wannan ya sa ake kallon karawar ta yau a matsayin mai matukar muhimmanci ga kungiyoyin guda 2, kuma dole daya daga cikin su ta fice daren yau.

A yanzu Chelsea tana bukatar cin kwallaye biyu kacal ta sauya makomar wasan.

Rahotanni sun ce Chelsea wadda ta lallasa Southampton da ci 6-0 a gasar Firimiya ba za ta samu damar amfani da ’yan wasanta irinsu Romelu Lukaku da Callum Hudson-Odoi da Ben Chilwell ba saboda raunukan da suka fama da shi.

Mai horar da ’yan wasan Madrid Carlo Ancelotti ya ce har yanzu da sauran aiki a gaban su kafin samun tikitin wasan kusa da na karshe a karawar yammacin yau.

A kuri’ar da galibin magoya bayan Chelsea suka kada, suna bayyana yan wasan da suke fatan ganin an fito da su da suka hada da: Edourdo Mendy, Antonio Rüdiger, Thiago Silva, Cesar Azpilicueta, Marcos Alonso, Mateo Kovačić, Ngolo Kanté, Reece James, Timo Werner , Kai Havertz da kuma Mason Mount.