MADUBI: Azumi cikin ‘azumi’ | Aminiya

MADUBI: Azumi cikin ‘azumi’

    BALARABE LADAN

A wannan shekarar azumin watan Ramadan ya zo wa Musulmin duk duniya a cikin mawuyacin hali da cutar coronavirus ta tura su a ciki, wanda ya sanya za su yi azumin a cikin halin kunci, domin har wadansu sun fara ‘azumin’ dole tun kafin watan Ramadan din ya shigo.

A duk shekara idan watan azumin Ramadan ya kama Musulmi sukan himmatu wajen ibada sosai tare da kokarin taimaka wa masu karamin karfi da kuma tashi tsaye wajen shirya tarurruka domin ilimantar da al’ummar Musulmi game da addininsu.

Wasu kungiyoyi da daidaikun mutane sukan raba wa Musulmi kayan abinci, wadansu kuma sukan shirya buda-baki ne su gayyato mutane.

Wadansu kuma sukan dauki nauyin karatu ko tafsiri ko lacca ne a kafofin yada labarai domin amfanin al’ummar Musulmi, wadansu kuma sukan dauki nauyin wadansu mutane zuwa Umarah a cikin watan azumin, da dai sauran ayyukan alheri da dama.

A bana ga dukkan alamu mutane kalilan ne za su iya ci gaba da ayyukan alherin da suka saba yi duk shekara, saboda cutar Kurona ta tsayar da harkoki sosai, ta yadda al’amura suka tsaya cik a fadin duniya, har ta kai ga mai bayarwa ya koma yana neman shi ma a ba shi.

Tun da cutar Kurona ta kunno kai take ta talauta al’umma, domin cuta ce da take son taruwar jama’a a wuri guda domin ta yi saurin yaduwa, saboda haka dole aka dauki matakin hana taruwar jama’a a wuri guda.

Hakan ya sanya an hana mutane fita su nemi abinci, domin an rufe kasuwanni da masana’antu da ma’aikatu da wuraren ibada, saboda haka hanyoyin samun abincin sun yi kadan.

Wannan ya jefa mutane a cikin mawuyacin hali da ya sanya mutane da dama suna wuni da yunwa kuma suna kwana da yunwa, saboda babu halin fita su je neman abin da za su ci, masu kokarin taimakawar kuma al’amarin yana neman ya fi karfinsu, saboda masu bukatar taimakon suna kara yawa sosai.

Domin a halin da ake ciki za ka ga wani kamar ya kamata ya taimaka ne, amma ida ka bincika sai ka tarar shi ma taimakon yake bukata, ya yi shiru ne kawai.

Ma’aikata da yawa suna cikin kuncin rayuwa, hakan ya shafi rayuwar masu sana’o’i da yawa, kamar teloli da masu walda da kanikawa da kafintoci da masu sayar da yadi da sauransu da yawa.

Masu darawa a wannan lokacin sai masu sayar da abinci da masu sayar da sinadarin tsabtace hannu da masu sayar da takunkumi da masu sayar da magunguna.

A bana an bayar da sanarwar cewa ba za a gudanar da tafsirai a wasu masallatan kasar nan ba, wannan yana nufin gidajen rediyo da talabijin da dama za su samu raguwar hanyar samun kudin shiga ke nan, don haka za su fuskanci matsala wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum, matsalar ta yi musu yawa ke nan, domin shigowar coronavirus ta takura harkokinsu, tunda an takura zirga-zirgar jama’a.

Haka al’amarin yake ga sauran ma’aikatu da kamfanoni, duk harkoki sun tsaya, masu kokari suna motsawa su ma karfin hali suke yi, domin suna gab da tsayawa, shi ya sanya talakawa suka kara tsunduma cikin halin kuncin rayuwa saboda hanyoyin samun abinci suna toshe.

Wadansu a kasuwanni suke samun abincinsu, yanzu kasuwannin a rufe suke, wuraren da ake budewa kasuwannin kuma babu masu ciniki sosai, saboda an rufe hanyoyi mutane ba za su iya zuwa cin kasuwar ba, wadanda suka samu zuwa kuma ana takura musu.

Wadansu kuma wuraren ibada suke zuwa, domin su sayar da kayansu, wadannsu kuma domin su nemi taimako a wurin ’yan uwansu, to yanzu an rufe wadannan wurare, an ce kowa ya zauna a gida, saboda haka ganin masu karfin da za su taimaka wa marasa karfi yanzu yana da wahala, domin sun shige gidajensu sun kulle, sai ’yan kalilan ne suke aikawa da sako.

Ba abin mamaki ba ne ka ji mutum ya kai Magariba bai ko karya ba, kuma a haka zai kwana, yanzu da azumin watan Ramadan ya zo a cikin irin wannan kunci zai ci gaba da azumin.

Saboda haka ya kamata mutane su daure su taimaka wa ’yan uwansu, domin yanayin da azumin bana ya zo ya sanya mutane suna cikin bukatar taimako fiye da kowane lokaci, duk da yake masu bukatar taimakon suna kara yawa, amma a daure a taimaka, domin mutane suna cikin wani yanayi na kuncin rayuwa.

Yanayin da ake ciki yanzu shi ne, idan an zauna a gida yunwa ta gallabi mutane, idan sun fita neman abinci coronavirus ta dumfare su, lamarin ya zamanto ‘ganmo na ci, kaya na ci ke nan.’ Allah Ya sawwake.

Tare Da

BALARABE LADAN

balaladan@yahoo.com