✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mafarauta Sun Cafke Masu Kai Wa Boko Haram Abinci

Mafarauta sun damke wasu da ke kai wa Boko Haram abinci da kuma wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kusa da…

Mafarauta sun damke wasu da ke kai wa Boko Haram abinci da kuma wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kusa da kauyukan Gorgor da Liya a Karamar Hukumar Hawul ta Jihar Borno.

Sun kuma kwato wata babbar bindiga da kudi kimanin N945,000 daga hannun masu garkuwa da mutane tare da mika wadanda ake zargin ga ofishin ’yan sanda da ke garin Azare a Karamar Hukumar Hawul domin ci gaba da daukar mataki.

Shugaban Kwamandan Mafarauta da ’Yan Banga a Yankin Arewa Maso Gabas (Sarkin Baka), Alhaji Mohammed Shawulu Yohanna ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri.

Alhaji Yohanna ya ce, rundunar ta kuma kama wasu da suke kai kayan abinci ga ’yan Boko Haram tare da kwato Naira miliyan shida a hannunsu a kauyen Gorgor, kafin a mika su ga Bataliyar Sojoji ta 231 da ke Biu domin ci gaba da daukar mataki.

Ya ce, rundunarsa ta gano masu garkuwa ne a wata rugar Fulani da ke Gorgor/Liya, inda suka kai farmaki a gidan shugabansu Fulanin.

Ya ce a lokacin da maharan suka gano cewa shugaban Fulanin ba ya nan, sai suka karya kafafun dansa, suka karbi kudi Naira miliyan daya daga hannun ’yan uwansa, duk da cewa baya nan, da kuma jikkata dansa.

Shugaban ya ce, “Mun samu labarin cewa wasu masu garkuwa da mutane sun kai farmaki wani matsugunin Fulani a tsakanin al’ummar Gorgor da Liya, nan take ni da jama’ata muka yi gaggawar zuwa yankin domin ceto.

“Da isa yankin, mun yi arangama da masu garkuwa da mutane da misalin karfe 3 na dare wanda ya kai ga musayar wuta, kuma mun yi nasarar shawo kansu, muka kama shugabansu wanda ke rike da wata babbar bindiga.

“Mun kuma kwato kudi kusan N945,000 daga hannun jagoran, saboda sun kashe wani kaso daga cikin Naira miliyan daya da suka kwace daga hannun Fulanin.

“A yanzu haka, mun kai shugaban da aka kama, kudin da aka gano da kuma bindigar zuwa Hawul, muka mika su ga jami’in ’yan sanda (DPO) don ci gaba da bincike,”  in ji Yohanna.

Daga nan sai ya yaba wa hukumomin tsaro da Gwamnatin Jihar Borno da kuma Kwamandan JTF Operation Hadin Kai (OPHK) da ke shiyyar Arewa Maso Gabas, Manjo-Janar Christopher Musa bisa jajircewarsu wajen gudanar aikin hadin gwiwa a yaki da rashin tsaro a jihar da ma yankin Arewa Maso Gabas.