✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mafarauta sun harbe gwanin kashe Zakuna da Giwaye

An tsinci gawarsa ce a kusa da babbar motarsa a kan hanyar Marken da ke yankin Limpopo.

Wani mafarauci da ke kashe giwaye da zakuna ya rasa ransa a kasar Afirka ta Kudu.

Mutumin mai suna Riaan Naude mai shekara 55 an tsinci gawarsa ce a kusa da babbar motarsa a kan hanyar Marken da ke yankin Limpopo, kuma an samu bindigar farauta guda da wasu kayayyaki.

Haka kuma, an samu gawar ce a kusa da wani wurin ajiyar namun daji na kasar.

Kafar labarai ta Moroela ce ta ruwaito labarin, inda ta ce a baya Naude ya sha sa hotunansa yana tsaye kusa da matattun namun daji, ciki har da zakuna da giwaye da rakuman ruwa.

Kakakin ’Yan sandan yankin, Mista Mamphaswa Seabi ya ce jami’ansa sun gano gawar ce bayan an kira su zuwa inda abin ya faru, Ya ce “Mutumin yana kwance a kan cikinsa kuma akwai jini a kansa da fuskarsa.’’

Sai dai Kungiyar Yaki da Cin Zarafin Namun Daji (HPG) ta yi ikirarin cewa, wani mutum ne ya harbe Naude, lokacin da ya tsayar da motarsa a kusa da Mokopane, bayan takaddama mai zafi a tsakaninsu.

An ce wasu mutum biyu ne suka fito daga cikin wata farar mota kirar Nissan suka harbe shi sannan suka sace bindigarsa daya suka tafi da ita.

Kuma wani makiyayin shanu ya ji karar harbin bindiga sai ya ga motar kirar Nissan tana gudu. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a wajen yin farauta.