✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mafi karancin albashi: ’Yan kwadago za su tsunduma yajin aiki a Nasarawa

Kungiyoyin kwadagon dai na zargin gwamnati ne da kin mutunta yarjejeniyar da suka cimma.

Gamayyar kungiyoyin kwadago a Jihar Nasarawa za su tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata, 15 ga watan Yunin 2021.

Za su fara yajin aikin ne saboda gaza aiwatar da yarjejeniyar mafi karancin albashi na N30,000 da suke zargin gwamnatin Jihar da yi da ma sauran batutuwa masu alaka da haka a Jihar.

Aminiya ta gano cewa matakin yajin aikin na zuwa ne bayan Majalisar Zartarwar kungiyoyin ta yi wani zama a ranar Litinin wanda ya dauki sa’o’i da dama.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen Jihar, Kwamared Yusuf Iya ya ce daukar matakin ya zama dole ne saboda kin mutunta bukatunsu da gwamnatin ta yi duk kuwa da bata uzuri har sau biyu da suka yi.

Ya ce wasu daga cikin bukatun nasu sun hada da kin aiwatar da karin mafi karancin albashi ba tare da wani kwakkwaran dalili ba da kuma kin karawa ma’aikata girma tun shekarar 2008.

Sauran bukatun sun hada da karin albashi na shekara-shekara, rashin bayar da horo ga ma’aikata, kin mayar da ma’aikatan wucin gadi da suka haura shekara 10 suna aiki na dindindin da dai sauransu.

Kwamared Yusuf ya ce, “Mun daga wa wannan gwamnatin mai ci kafa har na sama da shekara biyu amma ta yi kunnen uwar shegu da mu.

“Tun bakwai ga watan jiya ma ya kamata mu fara yajin aikin man amma saka bakin sarakunan gargajiya ya sa muka sake daga kafa.

“Amma duk da saka bakin, gwamnati ta ki yin abinda ya kamata, ba da gaske take ba.

“Mun gaji da gafara sa har yau bamu ga kaho ba, shi yasa muka yanke shawarar tsunduma yajin aiki saboda shi kadai ne yaren da gwamnatin ke fahimta,” inji shugaban ’yan kwadagon.