✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mafita daga zalunci da kunci (1)

A ’yan kwanakin nan sakonni da ke iske ni cikin akwatunan kafafen sada zumuntana sun zame mini abin taraddadi, cewa ake na bar rubutu kan…

A ’yan kwanakin nan sakonni da ke iske ni cikin akwatunan kafafen sada zumuntana sun zame mini abin taraddadi, cewa ake na bar rubutu kan matsalolin da ke addabar kasa ko al’ummarta, in na yi tsokaci bai wuce kan adabi ko makamantan haka. Wai me ke faruwa? Na sha ba da amsa, ba wani abu da ke faruwa, kawai dai gani na yi tamkar kira ne nake yi wa kurma ko kurame, ba a ji. Kuma ai ina jin gwargwado, an tabo kusan kowane bangare, kila jiran samun sauki ya rage. Wannan da wasu ne dalilina!

Alal misali mu koma kan batun irin halin kunci da wahalhalun da ’yan Najeriya suke ciki da kuma duba irin yadda duk da yawan addu’o’i da ake ta faman yi al’amura ba sa canjawa, shin me ya sa? Laifin wa ko su wa ne, shugabanni ko mu mabiya?

Sai dai kafin mu shiga cikin tattaunawar ka’in-da-na’in, bari mu soma da hikayoyi guda biyu na wata tsohuwa da kuma Hajjaju da ke cikin littafin Dare Dubu Da Daya domin su yi mana jagora.

A can zamanin da a kasashen Larabawa an bayar da labarin wani maniyyaci, wato mai haramar zuwa aikin Hajji, wata rana yana cikin ayari sai suka sauka a wani waje sai kuwa barci ya kwashe shi. Yayin da ya farka sai ya tarar ayari ya tafi, bai san inda suka nufa ba, ga shi duk guzurinsa da ya taho da shi yana can tare da su. A bisa haka ya ci gaba da tafiya a kasa har ya hango wata rumfa, ya karasa gare ta. Ya tarar da wata tsohuwa da kare a gabanta, yana barci. Lokacin kuwa yunwa ta ci karfinsa. Ya karasa gare ta, ya gaishe ta sannan ya roki abincin da zai ci. Tsohuwa ta ce, “Je ka wancan bigiren ka kamo kifi ka kawo min in soya maka in hada da abinci in ba ka.” Ya ce, “Ni kam ban iya farautar kifi ba.” Ta ce, “To je ka kamo maciji a wajen ka kawo min.” Ya ce, “Ni da ban iya farautar kifi ba ina zan iya ta maciji? Ya kara da cewa “Ni ban ma taba cin naman maciji ba.” Ta ce, “Mu je in kamo maka.”

Suka tafi kare na biye da ita suka kamo macizai da dama. Suka dawo ta soya masa su. Shi dai bai ga wani abinci ba bayan wannan, ga yunwa kuma na kwarzabarsa. Ta ba shi ya ci macizan sannan kishirwa ta sake dumfararsa. Ya tambayi ruwa, ta ce masa, “Je ka tafki ka sha.”

Ya tafi tafkin ya gan shi baki, kirin duk a cakude, amma da yake kishirwar ta tsananta gare shi, sai ya share wani wuri, ya kamfata, ya sha ruwan a haka, duk dacin da ke tattare da shi, ga shi babu dadi. Sannan ya dawo wurin tsohuwa ya ce mata, “Ina mamaki ya ke wannan tsohuwa da kika zabi zama a wannan wuri mai wahala, kina rayuwa daga wadannan abubuwa!” Ta ce, “Yaya abin yake kai a garinku?” Ya ce, “A garinmu ba haka muke rayuwa ba, muna da abinci mai kyau da ’ya’yan itatuwa masu zaki da ruwa mai dadi da naman tsuntsaye da na dabbobi, soyayye ko gasasshe ko dafaffe, sai wanda muka zaba.

Sannan ga abubuwan jin dadi nan barkatai sai ka ce a Aljanna wadda Allah Madaukakin Sarki Ya yi wa masu yi maSa da’a alkawari a Ranar Lahira.” Ta ce, “Duk na ji wannan, ina so ka fada min ko kuna da sarki ko shugaba wanda ke mulkinku bisa zalunci da son ransa. Haka kuma idan wani ya aikata laifi ya sa a kwace dukiyarsa a ruguza gidansa? Idan ma ya ga dama ya kore ku daga gidajenku ba tare da wani bahasi ba?” Ya ce, “Wannan kam akwai shi ko da a can kuwa.”

Ta ce, “To wallahi abincinku mai dadi da sauran abubuwan nishadi, matukar akwai zalunci da rashin tabbas sun zama guba da cuta. Mu kuwa abincinmu mara dadi, wanda ke tattare da adalci da tsantsar ’yanci da kwanciyar hankali magani ne a wurinmu. Ta kara da cewa ba ka ji ana cewa babbar ni’ima bayan samun shiga addinin Musulunci ita ce samun ’yanci da kwanciyar hankali ba?” Ta ce ai wadannan ni’imomi da ake maganarsu ba a samunsu sai a wajen shugaba adali, wanda ya amince cewa shi wakilin Allah ne a doron kasa, yana aiwatar da dokokinSa kamar yadda Ya umarce shi ba tare da son zuciya ba.

Ka sani sarakunan baya da wadansu shugabannin da suka gabata sun kasance masu son talakawa su matsowa kusa da su ne. Amma sarakunan yanzu da kuma shugabannin yau, sun fi fifita kama-karya, babu ruwansu da talakawa balle su taimake su.

Sai dai ka kara da lura, ka kuma kula, su ma jama’ar wannan zamani ba su zaman tamkar na baya ba. Yanzu ana wani irin zama ne a tsakanin jama’a mai cike da zargi da karya da rashin cikakkiyar magana. Yanzu zamani ya zama kowa so yake ya azurta kansa da karya ga kuma kekasasshiyar zuciya da ta mamaye mafi yawan al’umma. Ta ce ana biye wa son zuciya a halin yanzu, ana aiwatar da adawa da kiyayya. Duk sarki ko shugaba da ya zama haka, ko mutanensa suka kasance cikin wannan yanayi, to sai dai neman tsari a wajen Allah daga gare su.

Babu shakka rashin adalci ne sababin rugujewar daulolin da suka gabata. An fadi cewa zaluncin sarki ko shugaba na shekara dari bai kai zaluncin da talakawa ke yi tsakaninsu na shekara daya ba. Sai dai kuma an fadi cewa idan talakawa na zaluntar junansu, sai Allah Ya dora a kansu wani mugun sarki ko shugaba wanda zai hana su sakat. Don haka sai talakawa sun gyara tsakaninsu sannan za su samu adalin shugaba.

Za mu ci gaba