✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jikan Sardauna, Magajin Garin Sakkwato, ya rasu

Alhaji Hassan Danbaba ya rasu bayan rashin lafiyar kwana daya a Kaduna.

Allah Ya yi wa Magajin Garin Sakkwato kuma jikan Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello, wato  Alhaji Hassan Danbaba, rasuwa.

Alhaji Hassan Danbaba ya rasu ne a ranar 12 ga watan Farairu, 2022 bayan rashin lafiya ta kwana guda yana da shekara 54.

Daya daga cikin makusantan marigayin, wato Hassan Muhammad Binanchi, shi ne ya tabbatar cewa rasuwar ta auku ne a Jihar Kaduna bayan rashin lafiya da ta sami Magajin Garin Sakkwato a ranar Juma’a a sakamakon tuntube da ya yi a kafarsa.

Makusantan mamacin sun ce za a yi janazarsa a Jihar Sakkwato, bayan da aka kawo gawarsa.

Alhaji Hassan Danbaba ya rasu ya bar matan aure uku da ’ya’ya shida, mata hudu da  namiji daya.

Marigayin sanannen mutum ne a Nijeriya kuma jika ne ga Margayi Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello.

A watannin baya ne mahaifiyarsa, wato ’yar Sardauna, Hajiya Hafsa ta rasu.