✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maganin gargajiya ya yi ajalin mutum 10 ’yan gida daya

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada umarnin gudanar da bincike.

Wasu mutum 10 ’yan gida daya a garin Gwanara na Karamar Hukumar Baruten da ke Jihar Kwara, sun yi gamo da ajalinsu bayan kwankwadar wani maganin gargajiya.

Mummunan lamarin wanda ya faru tun a ranar Juma’ar da ta gabata ya bar mutanen al’ummar Biogberu cikin zullumi da tashin hankali.

  1. Karin kasafin N895bn: Majalisa ta kammala karatun farko
  2. Gwamnatin Kano ta rufe Asibitin Muhammadu Buhari

Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani daga rundunar ’yan sandan jihar dangane da faruwar lamarin.

Bayan tuntubar Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Karamar Hukumar Baruteen, Abdulrasheed Ibrahim, ya ce tun bayan samun labarin faruwar abun ya aike da tawaga zuwa yankin a ranar Talata don jin bahasi.

“Wajen yana da nisa sosai, amma mun aike da jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya don tabbatar da faruwar lamarin kuma har zuwa yau Laraba, muna dakon sakamakonsu.

“Bayanin da muke da shi, shi ne kabilar Fulani ne mutum 10 ’yan gida daya da suka sha maganin gargajiya kuma ya yi ajalinsu, da zarar tawagata ta dawo zan bayar da cikakken rahoton bincikensu.

Kakakin ’yan sandan jihar, Ayayi Okasanmi, ya tabbatar da cewar an kai musu rahoton faruwar lamarin.

“Bayan shan maganin gargajiya ’yan uwan junan su goma suka fara mutuwa daya bayan daya, ciki har da mahaifiyarsu da ke ciwon kafa.

“Kwamishinan ’yan sanda, Mohammed Lawal Bagega ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

“Ya kuma shawarci jama’a da suke zuwa asibiti ko neman shawarar likitoci kafin shan magani,” a cewarsa.