✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maganin matsalolin Najeriya na hannun majalisa -Boss Mustapha

'Yan Najeriya na son ganin Majalisar ta yi dokoki da za su magance matsalolinsu

Sakataren Gwanatin Tarayya Boss Mustapha ya ce mafita daga dukkannin matsalolin Najeriya na hannun Majalisar Tarayya.

Boss Mustapha ya ce dole ne ‘Yan Majalisar su sani cewa ‘yan Najeriya sun zura ido su ga irin matakai da dokoki da ‘Yan Majalisar za su yi domin magance matsalar tsaro da ta tattalin arziki da sauran matsalolin da ke damun kasar.

“Matsalolin na da yawa kuma ‘Yan Najerya na jira ku kawo musu mafita.

“Yanzu ne lokaci mafi kamata Majalisar ta yi wa kanta gyaran fuska domin biyan bukatun ‘yan Najeriya kasancewar shekara uku da ke tafe na da matukar muhimmanci ga Kasar nan”, inji shi.

Ya bayyana hakan ne a taron da Majalisar ta shirya wa ‘ya’yanta domin bitar batutuwan da ta sa a gaba a ranar Asabar a Abuja.