✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maganin matsalolin Najeriya na hannun ‘yan kasar —Uhomoibhi

Allah da kuma ’yan kasar ne za su taka rawar warware matsalolin, in ji Dokta Martin Uhomoibhi

Tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkin Al’umma na Majalisar Dinkin Duniya, Dokta Martin Uhomoibhi, ya ce duk mtasalolin da ke damun Najeriya da maganinsu na hannun ’yan kasar.

Ya bayyana wa taron wata kungiyar Kiristoci ta kasa (OSAN) a Abuja, ranar Juma’a, cewa kasancewar kaddarar kasar ba a hannun kowa take ba, ya sanya sai Allah da kuma ’yan kasar ne za su taka rawar warware matsalolin.

“Amurkawa su suka gina Amurka, Birtaniyawa suka raya Birtaniya, to Najeriya wa ake sa rai ya gina ta?

“Kasar Afirka ta Kudu za ta samu iko da karfi ne da babu Mandela?

“Amma sai da ya shafe shekaru 27 a gidan yari.

“Dubi kafuwar Rwanda; Mece ce ita a da, kafin rawar da Paul Kagame ya taka?”

A nasa bangaren shugaban Kungiyar OSAN, Chinedu Akabueze cewa ya yi idan ba a yi hankali ba, ’yan ubanci, da kabilanci ne za su kassara kasar baki daya.