Magidanci ya shiga hannu bayan kashe ’ya’yansa 3 | Aminiya

Magidanci ya shiga hannu bayan kashe ’ya’yansa 3

    Abubakar Muhammad Usman

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Enugu ta cafke wani magidanci bisa zargin sa da kashe ’ya’yansa cikinsa mata guda uku, sannan ya sanya su cikin firinji.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe ne ya sanar a ranar Laraba cewa lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Enugu ta Gabas.

Binciken ’yan sandan ya gano cewa mahaifiyar yaran ta je kasuwa tare da dansu namiji daya kacal, amma da ta dawo sai ta nemi ’ya’yanta mata ta rasa.

Matar ta zargi mijin nata bayan dawowarta daga kasuwa, ganin yadda ya rika yin wasu abubuwa da suka ja hankalinta.

Bayan ta duba da kyau, sai ta ga gawarwakinsu a cikin firinji da alamun duka a jikinsu.

Tuni aka garzaya da gawarwakin zuwa asibiti domin gano musabbabin mutuwarsu.

A halin yanzu dai ’yan sandan dai na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar wannan lamari.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abubakar Lawan, ya jajantawa mahaifiyar yaran, sannan ya ba ta tabbacin gudanar da bincike tare da yin adalci.