✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Iyalai miliyan 1.5 za su mallaki gidaje a Najeriya

Gwamnati za ta ba ’yan kasa rance su sayi gidaje miliyan 1.5 da za a gina masu saukin kudi

Magidanta akalla miliyan 1.5 ne za su mallaki gidaje masu saukin kudi da Gwamnatin Tarayya za ta gina a karkashin shirin habbaka tattalin arzikin kasa (ESP).

Da yake sanar da hakan a ranar Litinin, kwamitin samar da gidajen, ya ce gamnati za ta ba wa mutane bashin kudi mai karamin ruwa da ba ya bukatar bayar da jinginar kaddara domin su biya kudin gidajen.

’Yan kwamitin sun ce aikin wanda za a fara a farkon makon gobe zai lakume fiye da Naira biliyan 400 kuma an riga an zabi inda za a gina su.

Skara un da cewa an riga an zabi taswirar gine-ginen da za a yi don ganin masu daki 1 da 2 da kuma 3 ba su zarce naira miliyan daya da dubu dari takwas zuwa miliyan biyu ba.

A watan Yunin 2019, Kwamitin Zartaswa na Tarayya ya amince a raba Naira tiriliyan 2.3 ga ’yan kasa domin rage radadin asarar da suka tafka da kuma ceto tattalin arzikin kasa sakamakon rahoton da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya gabatar na ESC.

Haka kuma Shugaba Buhari ya umarci mataimakin nasa ya kula da aiwatar da shirin.