✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan APC da PDP sun yi taho-mu-gama kan lika fasta a Kwara 

Mutum daya ya samu mummunan rauni a kansa sakamakon arangamar da magoya bayan suka yi.

Ana zargin an jikkata wani mutum daya yayin da rikici ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da PDP a Jihar Kwara a kan lika fastar dan takara.

Lamarin da ya auku a unguwar Ode Alausa da ke Ilorin, an kuma bayyana cewa, an yi arangamar ce da muggan makamai.

Wani faifan bidiyo na lamarin da ya bayyana a kafafen sada zumunta a ranar Litinin, ya nuna yadda wata mata da ake zargin mai goyon bayan jam’iyyar PDP ce, ta zargi wani Alhaji Olosasa, jigo a jam’iyyar APC a yankin da jagorantar debo wasu ‘yan daba da kai wa ‘ya’yanta hudu hari saboda sun ki goyon bayan APC.

“A lokacin da ‘yan jam’iyyar APC ke lika fasta a alluna suka ga ‘ya’yana, Rashidi, Suraju da Muniru, ‘yan jam’iyyar su uku, sun bi su da duka. Kimanin su 12 sun yi wa dana na biyu kwanton bauna amma wasu mazauna yankin ne suka ceto shi.

“Daga baya suka fasa wa daya daga cikin ‘ya’yana [Sabit] kai da wani katon dutse har sai da ya suma. Da farko, mun yi tsammanin ya mutu har sai da muka isa asibiti,” mahaifiyar ta yi wannan ikirarin a cikin faifan bidiyon.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, Alhaji Olosasa ne ya umarci ‘ya’yansa da su far wa ’yan jam’iyyar PDP a lokacin da suke lika fastar PDP.

Da aka tuntubi shugaban jam’iyyar APC a jihar, Prince Sunday Fagbemi, ya musanta cewa mambobinsa ne suka aikata laifin.

Ya ce “An sanar mana da cewa sun ci zarafin mutane da yawa, amma muna kira ga jami’an tsaro da su kamo wadanda suka aikata laifin domin fuskantar doka.

Kakakin jam’iyyar PDP na jihar, Prince Tunji Morounfoye, ya shaida wa Aminiya cewa “Jam’iyyarmu na ci gaba da bincike amma ina tabbatar da cewa sun kawo mana hari kamar yadda aka gani bidiyon nan”.

A halin da ake ciki, kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, Ajayi Okasanmi a lokacin da yake mayar da martani kan lamarin, ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasa da su kira jan kunnen magoya bayansu domin dakile barna da tashe-tashen hankali.

Ya ce gargadin bai takaita ga wata jam’iyya ba, kuma bayanan sirrin da rundunar ta samu sun bayyana sunayen wadanda suka aikata laifin.

Ya kara da cewa “Wannan shi ne gargadi na karshe ga duk mai kokarin karya doka a Jihar Kwara saboda za su fuskanci hukunci sakamakon rashin bin doka da oda.”