✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magoya bayan Bolsonaro sun yi kutse a Majalisar Dokokin Brazil

Masu boren sun kuma yi yunkurin kutsawa harabar Kotun Kolin kasar da ma Fadar Shugaban Kasa.

Daruruwan magoya bayan tsohon Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro, sun yi kutse kan ginin Majalisar Dokokin kasar domin adawa da shugaba Luiz Inacio Lula da Silva.

Bayan shafe tsawon sa’o’i ana dauki ba dadi a Brazil, jami’an ’yan sanda sun sami nasarar kwantar da tarzomar da ta tashi bayan da masu zanga-zangar goyon bayan tsohon shugaban kasar suka mamaye ginin Majalisar Dokokin kasar.

Masu boren sun kuma yi yunkurin kutsawa harabar Kotun Kolin kasar da ma Fadar Shugaban Kasa da ke birnin Brasilia.

Alkalin alkalan kasar, Rosa Weber ta ce Kotun Kolin kasar za ta yi aiki wajen ganin hukunci ga ’yan ta’adda ya zama izina ga sauran jama’a.

A ranar Lahadi ne dai daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar Bolsonaro suka yi wa ginin Majalisar Dokokin kasar kutse tare da yin kira ga dakarun kasar da su kifar da gwamnatin shugaba Silva wanda ya sha rantsuwar kama aiki a makon da ya gabata.

Har yanzu dai magoya bayan tsohon shugaban kasar sun ki amincewa da shan kayen da Bolsonaro ya yi a zaben kasar, inda suke zargin cewa an tafka magudi.

Bolsonaro dai ya yi Allah wadai da kutsen da magoya bayansa suka yi a gine-ginen gwamnatin kasar tare da yin watsi da zargin da shugaba Lula ke masa na hannu a tayar da tarzomar.

Shugaba Lula ya sha alwashin daukar matakin shari’a ga duk wanda ke da hannu wajen ta da rikicin