✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan Super Eagles sun yi ajalin likita dan kasar Zambiya a Abuja

Dukan da magoya bayan Super Eagles suka yi masa ne sanadin ajalinsa

Magoya bayan Super Eagles sun yi ajalin wani likita dan asalin kasar Zambiya bayan da suka lakada masa dukan kawo wuka, bayan tashi daga wasan Najeriya da Ghana a Abuja.

Joseph Kabungo likita ne daga cikin jerin wadanda Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF), ta tura Abuja don sanya ido a kan wasan da aka yi tsakanin Super Eagles ta Najeriya da Black Stars ta Ghana ranar Talata.

Shi ne jami’in da CAF ta tura don yi wa ’yan wasa gwajin amfani da abubuwan kara kuzari a wasan Najeriya da Ghana da aka yi a filin wasa na M.K.O Abiola da ke Abuja.

Ya rasu bayan magoya bayan Super Eagles sun fusata tare da shiga cikin filin wasan.

Rahotanni sun ce magoya bayan sun lakada masa dukan da ya yi sanadin fita daga hayyacinsa.

Daga bisani an garzaya da shi asibiti don ba shi agaji, amma aka yi rashinsa sa’a rai ya yi halinsa.

Wani dan jaridar kasar Zambiya, Matimba Nkonje, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da mutuwar Kabungo a shafinsa na Twitter.

Tawagar ’yan wasan Super Eagles dai ta gaza zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022 da za a yi a kasar Qatar, bayan yin kunnen doki da Ghana.