Daily Trust Aminiya - Mahaifi ya kona ’ya’yansa saboda zargin maita
Subscribe

Godsgift Nyam da qanwarsa, Mary Nyam da ake zargin mahaifinsu ya qona saboda zargin maita

Mahaifi ya kona ’ya’yansa saboda zargin maita

Wani mutum mai suna Nyam Choji, da ke zaune a kauyen Shen a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato ya kona ’ya’yansa biyu Godsgift Nyam dan shekara 11 da kanwarsa Mary Nyam ’yar shekara 5 da ruwan zafi kan zargin maita a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, ASP Uba Gabriel ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce a labarin da suka samu, mahaifin yara da Mai unguwar wajen, suna da hannu wajen aikata wannan mummunan aiki.

ASP Uba Gabriel, ya ce tuni suka tura jami’ansu zuwa wajen don kamo dukkan wadanda suke da hannu wajen aikata wannan mummunan aiki.

Ya ce wadannan yara suna nan a raye kuma an kwantar da su a Asbitin Kwararru na Jihar Filato, da ke Jos domin yi musu jinya.

Shugabar Kungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya [NAWOJ] reshen Jihar Filato, Jennefa Yarima ta yi Allah wadai da faruwar lamarin, a wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce wannan abu wani mummunan take hakkin kananan yara ne. Don haka ta yi kira ga Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya tsaya wajen ganin an yi wa wadannan kanana yara adalci kan wannan abu da aka aikata musu.

More Stories