✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Mahaifin jarumi Umar Gombe ya rasu

Za a yi jana'izarsa a gobe Laraba da misalin karfe 10 na safe a Fadar Sarkin Gombe.

Allah Ya yi wa Alhaji Sani Labaran, mahaifin jarumi Umar Gombe rasuwa a yammacin ranar Talata.

Daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, Abba El-Mustapha ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Za a yi jana’izarsa a gobe Laraba da misalin karfe 10 na safe a Fadar Sarkin Gombe a Jihar Gombe.

Sanarwar ta yi addu’ar Allah Ya jikansa Ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma sa Aljanna ce makomarsa.

“Idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu cika da kyau da imani.”