✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin Nicki Minaj ya riga mu gidan gaskiya

Robert Maraj, mahaifin mawakiyar Amurka, Nicki Minaj, ya mutu a wani hatsarin mota irin na buge ni ka tsare da ya ritsa da shi a…

Robert Maraj, mahaifin mawakiyar Amurka, Nicki Minaj, ya mutu a wani hatsarin mota irin na buge ni ka tsare da ya ritsa da shi a birnin New York.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Mista Maraj yana tafe a kan hanyar da ke tsakanin titin Roslyn da Raffa a yayin da wata mota da ta fito daga Northbound ta buge shi kuma ta tsare.

Jami’an tsaro sun ce direban motar cikin hanzari ya kama gabansa ba tare da an iya samun wasu sahihan bayanai da za a iya gabatarwa a matsayin shaida ba.

Mista Maraj wanda a sanadiyar samun raunuka ya fita daga hayyacinsa, an garzaya da shi zuwa wani asibiti inda ya ce ga garinku nan a karshen makon da ya gabata kamar yadda TMZ online suka ruwaito.

Tuni dai jami’an reshen bincike laifukan da suka shafi kisan kai suka shiga sauke nauyin da rataya a wuyansu, inda suke neman al’umma sua agaza musu da duk wani bayani game da mai hannu a wannan aika-aika.

Nicki Minaj wacce tana daya daga cikin mawakan Hip Hop na Amurka da suka yi shura, har yanzu ba ta ce komai game da lamarin ba, a yayin da masoya da abokanan sana’ar da ma sauran wadanda suka shahara a duniye suke ta aike mata da sakon ta’aziyya dangane da rasuwar mahaifinta.