✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifin Sanata Ali Ndume ya rasu

Majalisar Dattawa ta dage zamanta na ranar Talata zuwa Laraba.

Alhaji Ali Buba Ndume, mahaifin Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya riga mu gidan gaskiya.

Sanatan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja, a ranar Talata.

Sanata Ndume, ya ce za a yi jana’izar mahaifinsa a ranar Talata, a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Sanarwar ta ce, “Muna amfani da wannan dama don nuna alhinin rasuwar Alhaji Ali Buba Ndume, mahaifin Sanata Mohammed Ali Ndume.

“Ya rasu a safiyar yau [Talata] a Maiduguri.

“Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin kan wannan rashin babba da aka yi.

“Za a yi jana’izar marigayi Alhaji Ali Buba Ndume, mahaifin Sanata Mohammed Ali Ndume da misalin karfe 4 na yamma a gidan Sanata Mohammed Ali Ndume, da ke titin Damboa kusa da ofishin NTA a Maiduguri.”

Aminiya ta ruwaito cewa, domin nuna alhinin wannan rashi da aka yi, Majalisar Dattawa ta dage zamanta na ranar Talata zuwa Laraba.

Sanata Ajayi Boroffice ne ya gabatar da kudirin dage zaman.