✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Babban Editan Daily Trust ta rasu

Za a yi jana’izarta da karfe 8:00 na safiyar Litinin a Kano.

Mahaifiyar babban editan jaridar Daily Trust, Naziru Mika’ilu Abubakar, wato Hajiya Rakiya Abubakar ta rasu.

Marigariyar ta rasu ne da yammacin Lahadi a gidanta dake unguwar Koki a birnin Kano.

Da yake tabbatar da rasuwar a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, Malam Naziru ya rubuta, “Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Raji’un. Allah ya yi wa mahaifiyarmu rasuwa yau [Lahadi] da yamma.

“Za a yi jana’izarta a unguwar Koki, bayan masallacin Gwani Danzarga da misalin karfe takwas na safiyar ranar Litinin.

“Allah ya jikan Inna da rahama da sauran iyayenmu, ya kuma hada mu da su a Aljannar Firdausil Aalaa. Ameen.”