✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Adamawa ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa, Crowther Seth ta rasu. Mama Metusudo Helima Seth mai shekara 118 ta rasu ne a ranar…

Allah Ya yi wa mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa, Crowther Seth ta rasu.

Mama Metusudo Helima Seth mai shekara 118 ta rasu ne a ranar Talata a gidanta da ke garin Lamurde.

Sakatare Watsa Labaran Mataimakin Gwamnan, George Kushi ya ce dattijuwar wadda aka sha rade-radin cewa ta mutu, ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya mai alaka da tsufa.

Sanarwar ta ce za a binne mamaciyar a ranar 17 ga Oktoba, 2020 a Lamurde kamar yadda addinin Kirista ya tanadar.

Mama Metusudo Helima ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki da kuma tattaba kunne masu yawan gaske.