Mahara sun bindige dan sanda a Ondo | Aminiya

Mahara sun bindige dan sanda a Ondo

Jami’in Dan Sandan Najeriya
Jami’in Dan Sandan Najeriya
    Abubakar Muhammad Usman

Wasu ’yan bindiga a kan babura sun harbe wani dan sanda har lahira a yayin da yake bakin aiki a Jihar Ondo, sannan suka tsere.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Funmilayo Odunlami, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, wanda ta ce ya faru ne a yankin Oka-Akoko da ke Karamar Hukumar Akoko ta Yamma.

Sai dai ba ta bayyana sunan dan sandan da ya rasa ran nasa ba a hannun maharan.

Lamarin da ya faru a ranar Talata ya jefa mazauna yankin cikin rudani da firgici.

Kakakin ’yan sandan ta ce tuni rundunar ta fara bincike don gano wadanda kashe dan sandan.

A cewarta bincike ya yi nisa, kuma da zarar an kammala za su sanar da jama’a halin da ake ciki.

“A yanzu muna matakin farko na bincike, kuma mun fara samun bayanan da suka dace; Da zarar mun kammala za mu bayar da sanarwar halin da ake ciki; Wadanda suka aikata laifin kuma, nan bada jimawa ba za su shiga hannu,” a cewarta.