✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun bindige mutum 55 a Nijar

Mutum 55 sun kwanta dama a harin ’yan bindiga a yankin Tilleberi.

Mutum 55 sun kwanta dama a wani harin ’yan bindiga a yankin Tilleberi na Jamhuriyar Nijar.

Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwana uku daga ranar Laraba saboda rasuwar, sakamakon harin na ranar Litinin a yankin Tilleberi mai makwabtaka da iyakar kasar Mali.

Majiyoyi sun ce maharan sun yi luguden wuta ne a kan fasinjoji da ke hanyarsu ta komawa gida daga kasuwa sannan suka cinna wa motar wuta.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayane game da maharan, sai dai mayakan jihadi na Boko Haram, ISWAP da dangoginsu sun addabi yankin Sahel.

Ko a watan Janairu sai da aka kashe aƙalla mazauna wani ƙauye 100 a wani harin Jihadi.

(Daga BBC)