✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun bindige shanu 10 a Filato

Kwanaki kadan bayan an bude wuta a kan wasu shanu a yankin Riyom.

Wasu mahara sun bindige shanu 10 a yankin Tashan Maude da ke kan hanyar Rafin Bauna a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

Shguaban Kungiyar Cigaban Fulani ta Gan Allah (GAFDAN), Garba Abdullahi Muhammad, ya ce a ranar Juma’a da almuru ne aka bude wa shanun wuta a lokacin da suke kiwo.

“Kafin wannan an kashe shanu 10 an jikkata 23.  Ranar Juma’a an kara kashe 10. Da gangan ake yi domin tunzura mu. Mun kai kara Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Bassa da kuma Rundunar Tsaro ta Operation Save Haven,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar matakan da suka dace domin magance matsalar.

Da yake magana kan harin, kakakin rundunar tsaro ta Operation Save Haven, Manjo Ishaku Takwa, ya ce shanu shida ne suka mutu a harin na ranar Juma’a.

Al’ummomin Fulani da Irigwe dai na yawan zargin juna da kai hare-hare a kauyukan Karamar Hukumar ta Bassa.

Kimanin mako guda ke nan da wasu mahara suka bindige wasu shanu 10 tare da jikkata wasu 23 a lokacin da suke tsaka da kiwo a kauyen Waren da ke Karamar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.

Bayan karuwar hare-haren a kwanan nan ne Babban Kwamandan Rundunar Operation Save Haven, Manjo-Janar Ibrahim Ali, ya kaddamar da kwamitin zaman lafiya na hadin gwiwa mai mambobi 36  a ranar 12 ga watan Satumba da muke ciki.

An dora wa kwamitin zaman lafiyan alhakin lalubo hanyoyin kawo karshen hare-hare da ramuwar gayya da ake samu a kananan hukumomin Riyom da Jos ta Kudu da kuma Bassa a jihar ta Filato.