✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mutum 11 a kudancin Kaduna

Sun kashe mutum daya tare da sace kayayyakin jama’a yayin harin

Wasu mahara sun kai farmaki a kauyukan Kabode da Ankuwa da ke da nisan kilomita 10 daga garin Kachia, a Kudancin Jihar Kaduna tare da sace musu kayayyaki.

Majiyar Aminiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce maharan sun shiga yankunan ne a kan babura da yawa da misalin karfe 9:20 na dare, sannan suka fara bude wuta kan mai uwa da wabi.

Zuwa yanzu adadin wadanda aka kashe sun kai mutum 11 daga kauyukan Ambrum da Ankuwa da Kabode da kuma wata rugar Fulani.

Majiyar ta kara tabbatar wa Aminiya cewa an yi ba-ta-kashi tsakaninsu da sojoji inda zuwa yanzu aka kora ’yan bindigar da ake jin sun tafi da wadanda aka kashe musu.

Majiyar ta ce, “Wannan shine karo na biyar tun shekarar da ta gabata da maharan ke kawo mana hari suna karbar kudin fansa.

“A baya ma sai da suka saka mana biya harajin biyan har Naira miliyan biyar kan ba za su sake kawo mana hari ba, sai ga shi sun dawo bayan an ba su abinda suka bukata,” inji majiyar.

Zuwa yanzu dai, mutanen yankunan na ta yin kaura suna barin gidajensu don tsira da rayukansu.

Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai amsa wayar sa ba kuma bai amsa rubutaccen sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya tura masa ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.