✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun hallaka mutum 6 a Imo

Sun budue wa mutane wuta a wuraren sana'arsu.

Wasu mahara da ake zato ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kashe mutum shida a garin Owerri, hedikwatar Jihar Imo.

Wani mazaunin garin, Muhammad Sani Mairago, ya shaida wa Aminiya cewa, “Haka siddan wasu mahara suka kashe mutum shida a garin Owerri ranar Juma’a da dare a lokacin da mutanen suke bakin kasuwancinsu, uku ’yan Arewa ne sauran ukun kuma ’yan asalin jihar ne.”

Ya ci gaba da cewa, “Mutum ukun ’yan Arewa ne masu sana’ar sayar da nama sun ka kona babura da aka kiyasta za su kai kamar guda talatin.”

Jihar Imo na daga cikin jihohin Kudu maso Gabas da ake samun yawan kai hari ga al’umma da ofisoshin ’yan sanda.

Wakilinmu ya tuntubi ofishin ’yan sandan jihar game da lamarin harin amma babu wanda ya ce masa uffan.