✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun harbe mutum 5 a kauyen Filato

Mutum biyar sun rasu a wani harin ’yan bindiga da sanyin safiya a Karamar Hukumar Jos ta Gabas, Jihar Filato.

Mutum biyar sun rasu a wani harin ’yan bindiga da sanyin safiya a Karamar Hukumar Jos ta Gabas ta Jihar Filato.

Dandazon ’yan bindiga sun shiga kauyen Fobur a lokacin mazauna ke barci, kafin wayewar garin Juma’a, suna harbe-harbe, har suka kashe mutum biyar.

Majiyarmu a kauyen ta ce mutum na farko da aka kashe a kauyen ya gamu da ajalinsa ne nan take bayan ya leko domin tabbatar da abin da ke faruwa.

Daga nan maharan suka biya ta kuayen Fusa, inda suka yi garkuwa da wani mai suna Haruna Ajik.

Maharan sun kuma kashe wasu mutum biyu a kusa da wata makarantar firamare daura da kauyen Fobur, da wasu biyu a wani wuri mai suna Naton.

Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sanar da su ne bayan bata-garin sun yi aika-aikar sun tsere.

Ya ce DPO na yankin ya sanar da rundunar tsaro da Operation Safe Have, wadda ta tura karin jam’ianta zuwa yankin domin taimaka wa mahfaruta da ’yan banga.

Jami’in ya ce zuwa lokacin ba a san dalilin harin ba, kuma yankin ba ya fama da wani rikici, amma ana bin sawun maharan.