✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kai farmaki ofishin ’yan sanda a Anambra

Maharan sun yi awon gaba da makamai daga ofishin 'yan sandan.

’Yan Sanda a Jihar Anambra sun dakile farmakin da mahara suka kai kan ofishinsu da ke Nnewi da ke kan hanyar Okigwe a yankin Umudim, Nnewi.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa jami’an sun yi fatattaki maharan da suka zo cikin motoci da tsakar rana.

  1. Kotu ta yanke wa barawo hukuncin bulala 12
  2. Budurwa ta banka wa kawarta wuta kan sabani

Ikenga ya ce ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kai dauki matakan tabbatar da cewa an samu cikakken tsaro a Jihar ta Anambra.

Amma, wani mazaunin yankin da aka sakaya sunansa ya shaida wa NAN cewa sun ji karar harbin manyan bindigogi a kusa da yankin da misalin karfe biyu na dare ranar Litinin.

“Mun ji harbe-harbe tsakanin wadanda muke zargin ’yan bindiga ne da kuma ’yan sanda a Nnewi kuma hakan ya haifar da tashin hankali tsakanin mazauna yankin,” inji shi.

Majiyar ta kara da cewa ’yan bindigar sun shigo a cikin motoci kimamin bakwai zuwa ofishin ’yan sandan, inda suka fara harbi, aka dauki sama da awa daya ana luguden wuta.

Sai dai an rawaito cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da makamai a ofishin ’yan sandan.

Kakakin ’yan sandan ya ce bayan samun karin dakaru daga rundunar ’yan sandan jihar, maharan sun tsere da suka ga za a ci karfinsu.