✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe babban dan Sanata Bala Na’Allah

A kwanan nan Kyaftin Abdulkarim Na’Allah ya shiga daga ciki.

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun tabbatar da cewa, an yi kicibus da gawar babban dan Sanata Bala Ibn Na’Allah har uwar daka a gidansa da ke Unguwar Malali ta Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kyaftin Abdulkarim Na’Allah mai shekara 36 wanda matukin jirgin sama ne a kwanan ya shiga daga ciki.

Bayanai sun ce wadanda suka kashe shi ta hanyar makara sun yi masa dauri irin na tumu da igiya sannan suka yi awon gaba da motarsa da wasu kayayyaki.

Mashawarci na musamman ga Sanata Na’Allah, Garba Muhammad, yayin tabbatar da mummunan abin da ya faru, ya ce maharan sun shiga gidan ne ta rufin kwanon sama da ke kusurwar bayan gidan sannan suka dira har dakin kwanan mamacin.

Ya ce wani mai gadi a makwabta ne ya ankarar da jama’a bayan ya lura da kofar gidan mamacin a bude sabanin yadda ya saba gani.

Da yake zantawa da Aminiya, Malam Garba ya ce za a yi jana’izar mamacin a kan titin Yahaya sannan za a binne shi a makabartar da ke Unguwar Sarki.

Har ya zuwa yanzu dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta ce uffan a kan lamarin ba, sai dai Malam Garba ya ce an sanar da ita kuma jami’anta tuni sun hallara a gidan da lamarin ya auku.

Bala Na’Allah wanda ke zaman Sanatan shiyyar Kebbi ta Kudu a zauren Majalisar Dattawa, a halin yanzu ya yi balaguro zuwa ketare.