✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe jami’an tsaro sun sace mutane a Kaduna

Maharan sun rika shiga cikin gidaje suna kama mutane su tafi da su

Jami’an tsaron JTF biyu sun rasu a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai unguwar Sabon Gero da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutane da dama a yankin, ciki har da wani mai shagon sayar da magunguna da matarsa.
Wata ganau ta ce, “Muna cikin yin wasu aikace-aikace da tsakar dare sai muka ji sun fara harbe-harbe
“’Yan bindigar sun rika balla gidaje suna shiga su kwashi mutane, a yayin da mutane ke ta kokarin tserewa.”
Maharan sun yi wa yankin Sabon Gero dirar mikiya ne da misalin karfe daya na dare, kafin wayewar garin ranar Laraba.
Aminiya ta samu bayanai cewa shida daga cikin mutanen da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su da farko sun samu sun kubuta.
An kai harin ne kwanaki kadan bayan ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutum bakwai, ciki har da matar wani soja, a unguwannin Keke A da Keke Ba da ke makwabtaka da Sabon Gero.