✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe magidanci sun sace ’ya’yansa 3 a Zariya

’Yan bindiga sun kashe wani magidanci sannan suka yi garkuwa da ’ya’yansa uku a unguwar Sayen Lemu da ke yankin Dutsen Abba Karamar Hukumar Zariya.…

’Yan bindiga sun kashe wani magidanci sannan suka yi garkuwa da ’ya’yansa uku a unguwar Sayen Lemu da ke yankin Dutsen Abba Karamar Hukumar Zariya.

Maharan sun shiga gidan magidancin mai suna Alhaji Habibu ne da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba, suka kashe shi sannan suka tafi ’ya’yan nasa.

Wurin da aka kai harin ba shi da nisa sosai da Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke kan Babbar Hanyar Zariya zuwa Kaduna a yankin Zariya.

Harin na zuwa ne bayan ’yan bindiga suka tare hanyar Kaduna zuwa Kaduna a ranar Litinin, suka bindige mutum uku ciki har da wani dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Ridwanu Gadagau.

Wata majiya a unguwar ta ce, “Ba ma zaton ’yan ina da kisa ne, mun fi zaton ’yan bindiga ne da a baya-bayan nan suka addabi unguwar.

“Ka san yanzu kimnain shekara daya ke nan da ’yan bindiga suka matsa wa unguwarmu da hare-hare, amma har yanzu babu wani kwakkwaran mataki da aka dauka domin kare rayukan jama’a.”