✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mahalarta daurin aure 7 a Imo

Maharan sun bude wa mahalarta daurin aure wuta a kan hanyarsu ta komawa gida.

An shiga rudani da firgici bayan an samu labarin cewa wasu ’yan bindiga da ake zargin dakarun Ebubeagu ne, sun kashe wasu mutum bakwai da suka halarci wani daurin aure a yankin Awomama da ke Karamar Hukumar Oru ta Yamma a Jihar Imo.

Wakilinmu ya rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, yayin da wadanda abin ya rutsa ke komawa kauyensu da ke Otulu na Karamar Hukumar Oru ta Gabas lokacin da ’yan bindigar suka bude musu wuta.

Shugaban al’ummar Otulu, Nnamdi Agbor, ya shaida wa manema labarai cewa mutane bakwai ne suka mutu nan take yayin da wasu kuma ba a san inda suka shiga ba.

Ya ce, “A lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida mahara  Ebubeagu da suka hange su a kan babura sun bude musu wuta; Kamar yadda na sanar da ku, mun gano gawarwakin mutum bakwai.

“Mutum biyar sun bace, yayin da biyu kuma suka samu munanan raunuka,” a cewarsa.

Bayanai sun ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mohammed Ahmed Barde ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ’yan sanda sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.