✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara Sun Kashe Mutum 1 Sun Sace Wasu 3 A Zariya

Wasu gungun mahara sun hallaka mutum daya, sun kuma dauke mutane uku a daren Talata sa'ilin da suka kai harin a unguwar Wusasa da ke…

Wasu gungun mahara sun hallaka mutum daya, sun kuma dauke mutane uku a daren Talata sa’ilin da suka kai harin a unguwar Wusasa da ke Zariya.

Maharan sun dira unguwar ne da misalin karfe 10 na dare, suka je gidan wani wani Dokta Oderinde suna harbe-harbe, suna kokarin balla kofar gidan amma hakan bai yiwu ba.

Dakacin Wusasa, Injiniya Isiyaku Yusuf, wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin, ya ce lokacin da suke kokarin balle kofar maigidan sai wani dan haya mai suna Oluwakemi Israel Oluwatosin a gidan ya leko don ganin abin da ke faruwa.

“Ganin maharan dauke da bindigogi sai ya koma dakin shi ya kulle kofa, hakan yasa ’yan bindigar suka harbi kofar dakinsa, inda aka yi rashin nasara, yana boye a bayan kofa nan take suka same shi a kirji inda rai ya yi halinsa.

“Bayan sun harbe dan hayar, sai suka fito daga gidan sukayi awon gaba da wasu matasa uku da suka hada da Douglas Silas, Treasure Yohanna Victor da kuma dan maigidan, mai suna Precious Oderinde,” in ji dagajin.

Ya ce lokacin da ya sami labarin ’yan bindigar ya kira jami’an tsaro, kuma sun zo jim kadan bayan maharan sun arce da mutanen da suka sace.

Ya kara da cewa DPO da jami’ansa tare da ’yan sintiri sun yi kokarin bin maharan har Dutsen Kufena inda suka yi ta nema amma ba su sami ganin su ba.

Injiniya Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa kan bangaren shari’a wanda ya zarga da sakin wasu “masu yi wa ‘yan bindiga leken asiri” a yankin bayan kuma sun amsa laifinsu na gayyatar ’yan bindiga zuwa yankin.

Ya ce ya zuwa yanzu mutane bakwai aka kashe a yankin sakamakon ayyukan ’yan ta’adda a yankin, baya ga wadanda aka sace da dama.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce yana halarta taro a lokacin da wakilinmu ya tuntube shi, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.