✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 105, sun kora 12,753 a Sokoto

Jihar Sokoto ta rasa rayuka 105 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka tilasta wa wasu 12,753 gudun hijira a Karamar Hukumar Birnin Magaji a cikin…

Jihar Sokoto ta rasa rayuka 105 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka tilasta wa wasu 12,753 gudun hijira a Karamar Hukumar Birnin Magaji a cikin wata biyu.

Kananan yara 6,377‬ ne ke cikin ‘yan gudun hijira daga Birnin Magaji, inda ‘yan ta’adda suka kai hari a kauyuka goma, a cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA).

Darekta Janar din SEMA Nasiru Aliyu ya ce mutum 60,000 ne ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar Sokoto.

Mutanen, a cewarsa sun yi kaura ne bayan ‘yan bindiga sun tayar da garuruwansu a jihar ta Sokoto da kuma jihohin Zamfara da Katsina da kuma Jamhuriyar Nihar.

“Gwamnati na kulawa da su tana ba su abinci da magunguna da sauran bukatu”, ya ce.