✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 11 a Kaduna

’Yan bindiga sun kashe karin mutum 11 a yankunan Jihar Kaduna

’Yan bindiga sun kai wa wasu kauyuka hari suka kashe mutum 11 a Kananan Hukumomin Igabi da Kajuru na Jihar Kaduna.

’Yan bindiga sun far wa garin Marabar Kujuru ne ranar Lahadi da dare sannan aka kai wa kauyen Albasu hari a ranar Litinin.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya ce, “Ranar Litinin ’yan fashin daji sun kai hari a kauyen Albasu kusa da Dajin Malum a yankin Sabon Birnin suka kashe wasu mazauna; ranar Lahadi kuma sun far wa Maraban Kajuru suka sace mutum biyu suka kuma kashe wani mutum kafin su tsere ta cikin jeji”.

Mazauna garin kauyen Albasu sun shaida wa Aminiya cewa maharan sun kashe mutum 11 suka kona gidajen jama’a sannan suka yi awon gaba da shanunsu.

Kashe-kashen na zuwa ne bayan ruhoton mahara sun kashe mutum 15 a kan hanyar Abuja daga Kaduna suka kuma yi garkuwa da wasu da dama.

Gwamnain Jihar Kaduna ta ce hukumomin tsaro na bin sahun ‘yan fahin a yankunan na Igabi da Kajuru.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya mika sakon ta’aziya zuwa ga iyalan mamatan tare yi musu addu’ar samun rahama”, inji Aruwan.

Ya ce sojoji da ke sintiri sun gano gawar wani dan bindiga da ya rasu sakamakon raunin bindiga wanda suka gano bindiga kirar AK47 da wasu kayan amfani a kusa da gawarsa da ta rube.