✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 2, sun sace 9 a Sabon Birni

’Yan binidgar sun kai harin ne don daukar fansar kashe musu mutane da aka yi.

Akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a hannun wasu mahara da suka sace wasu mutum tara a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Majiyarmu ta shaida mana cewa maharan sun kai hari ne a kauyen Marakawa a ranar Talata, inda suka kashe mutum biyu sannan suka yi awon gaba da mutum biyar.

A ranar Laraba kuma suka kai farmaki kauyen Makuwana suka yi garkuwa da mutum hudu.

Wakilinmu ya rawaito cewa maharan sun kuma yi kokarin shiga wasu kauyuka da ke Karamar Hukumar Wurno ta jihar, amma ba su soji da ’yan banga da ke yankin suka yi musu luguden wuta suka fatattake su.

Shugaban Karamar Hukumar, Abubakar Arzika, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce maharan na kai farmakin ne don daukar fansar mutum biyu da aka kashe daga cikinsu a wasu yankuna na karamar hukumar makonni biyu da suka shude.

“Ba su yi nasara ba saboda zuwan dakarun soji da ’yan banga, sakamakon ankarar da su da mazauna kauyen suka yi,” a cewarsa.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.