✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 3 a Binuwai 

Maharan sun yi wa mutanen kwanton bauna sannan suka kashe su.

Wasu mahara dauke da muggan makamai sun kashe mutum uku a yankin Tse-Ikem da ke Karamar hukumar Logo ta Jihar Benuwai. 

Wani shugaban al’ummar yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho a ranar Litinin, cewa sun rika jin karar harbe-harbe, a kusa da kauyen Arufu, kuma ya haifar da rudani a yankin.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6, “A ranar Lahadi 23 ga Oktoba, 2022 da misalin karfe 6 na yamma, inda wasu makiyaya dauke da makamai suka kashe Mista Aondona Saai da Mista Avalumun Ukerchia Adaa dukkansu mazauna Tse-Igbur da ke mazabar Ukemberagya na Ukemberagya/Tswarev a Karamar Hukumar Logo a kusa da unguwar Anawah tsakanin Titin Chembe da Anyiin.”

Shugaban Karamar Hukumar Logo, Salome Tor, wanda ya tabbatar da kisan mutum ukun, ya ce lamarin ya rutsa da wani matashi ne a ranar Juma’a yayin da aka kashe sauran mutum biyu a ranar Lahadi.

“A ranar Lahadi da misalin karfe 5 na yamma wasu wasu makiyaya dauke da makamai suka yi wa wasu mutum biyu a kan babur tare da wata mace kwanton bauna, amma sun kyale matar ta shiga daji a guje, ta haka ne muka samu labarin abin da ya faru.

“Ana zabar mutanen da ake kashewa ne kuma mafi yawan wadanda ake kashewa maza ne, domin muna da manyan jami’an tsaro.

“Ko a ranar Juma’a sun kashe wani matashi tare da kone babur dinsa,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho.

Shugaban ya kara da cewa, “Mutanenmu manoma ne amma ba za su iya zuwa gonaki ba a yanzu, wadannan (makiyaya da ke dauke da makamai) sukan kawo shanu su cinye musu amfanin gona.

“A wasu lokutan sukan bari sai mata sun girbe doya sai maharan su diro daga kan bishiya su tilasta matan su sauke doyar tare da yankawa dabobbinsu domin su ci.”

Da aka tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.