Mahara sun kashe mutum 4, sun sace 50 a Zamfara | Aminiya

Mahara sun kashe mutum 4, sun sace 50 a Zamfara

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga
    Abubakar Muhammad Usman

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da kisan mutum hudu tare da yin garkuwa da mutum 50 a garin Goran Namaye da ke Karamar Hukumar Maradun ta jihar.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka yayin tattauna wa da manema labarai ranar Litinin a Gusau, babban birnin Jihar.

Shehu, ya ce ‘yan bindigar sun farmaki garin cikin daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu sannan suka sace wasu mutum 50.

Sai dai ya ce an tura jami’an tsaro yankin don daukar matakan tsaro da suka dace.

A cewarsa, Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Zamfara, CP Yakubu Elkana, ya ba da umarnin ceto wanda aka yi garkuwa da su.

Kwamishinan ya umarci jama’ar yankin da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce jami’an tsaro na aiki don tabbatar an kubutar da wanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.