✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum daya, sun kona gidaje da motoci a Zangon Kataf

Maharan sun kuma kona gidaje shida da motoci uku.

An kashe wani yaro mai kimanin shekara shida da haihuwa mai suna Salisu Danjuma tare da jikkata wani mutum daya a wani hari da aka kai garin Zango da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.

Maharan da suka kai harin da misalin karfe 2:25 na daren Juma’a sun kuma kona gidaje shida da motoci uku, kamar yadda wata majiya a garin ta tabbatar wa da Aminiya.

Majiyar ta kara da cewa bayan shigowar maharan ba su yi wata-wata ba suka fara harbe-harben bindiga tare da cinna wa gidaje wuta.

Daya daga cikin motocin da aka kona a Zangon Kataf
Daya daga cikin motocin da aka kona a Zangon Kataf
GWani gidan da aka kona aZangon Kataf
GWani gidan da aka kona aZangon Kataf

Shi ma wani mazaunin garin na Zango, Nura Bako, ya shaida wa Aminiya cewa suna zargin wata kungiya mai fada a ji a yankin da kai harin wacce ya ce a ko da yaushe ta fitar da takardar manema labarai sai ta zargi mutanen garin da bai wa ’yan bindiga mafaka a duk lokacin da aka kai wa wata kabila hari.

A karshe yayi kira ga gwamnati da ta samar wa da mutanen garin Zango tsaro ta hanyar gyara tsohon barikin ’yan sanda da aka yi watsi da shi a garin, tare da gina barikin soji don dakile mummumar barazanar da ya ce suna fuskanta.

Sai dai yayin da wakilin Aminiya ya tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai same shi ta waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.