✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe shanu 10, sun raunata 23 a Filato

Miyetti-Allah na neman a hukunta maharan sannan a biya mambominta diyya.

Wasu ’yan bindiga a daren Alhamis sun hallaka akalla shanu guda 10 suka jikkata wasu 23 lokacin da suke kiwo a kauyen Waren da ke Karamar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.

Abdullahi Yusuf Ibrahim, Sakataren kungiyar Miyetti-Allah a Jihar shi ne ya tabbatar da kai harin ranar Juma’a.

Ya ce sun kai rahoton harin ga ofishin ’yan sanda da ke Riyom da kuma na rundunar tsaro ta Operation Safe Heaven da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Sai dai kungiyar ta yi kira ga jami’an tsaro da gwamnatin Karamar Hukumar da ma ta Jihar da su zakulo wadanda suka aikata ta’asar sannan su biya su diyya.

Sakataren ya ce, “Bama son mu sami matsala da kowa. Zaman lafiya muke so saboda ba ta yadda za mu sami ci gaba in babu shi.

“Ba mu yi wa wadanda suka yi mana wannan aika-aikar komai ba. Saboda haka, don samun zaman lafiya, muna kira ga hukumomi da su kama wadanda suka kai mana hari su hukunta su sannan mu kuma su biya mu diyya saboda da gangan aka kai mana harin.”

Aminiya ta rawaito cewa a ’yan makonnin nan, ana yawan samun kai sabbin hare-hare da kuma na ramuwar gayya a Jihar, wacce dama ta yi kaurin-suna wajen tashin-tashina mai alaka da kabilanci da addini.

Gwamnatin Jihar dai ta sha kiran bangarorin rikicin domin tattaunawa, amma har yanzu ga alama kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, ASP Ubah Gabriel, bai amsa kira da kuma rubutaccen sakon da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.