✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe shugaban dalibai a Kaduna

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi sanadin ajalin shugaban kungiyar daliban Rigasa a jihar Kaduna.

‘Yan bindiga ne sun kashe tsohon Shugaban Kungiyar Daliban Rigasa, Kaduna, Kwamared Auwal Rabiu Daura a tashar jirgin kasa.

‘Yan bindigar sun ji wa mutum daya rauni sannan suka yi garkuwa da wani mutum daya a lokacin harin.

Mutane ukum na cikin abin hawa yayin da ‘yan bindigar suka bude musu wuta a ranar Juma’a, daura da tashar jirgin kasa da ke Rigasa a garin Kaduna.

Yanzu haka Umar bn El-Khatab yana Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna, inda ake ci gaba da ba shi kulawa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin Abdul’Azeez Madugu (Dam Dubai), ya ce an yi jana’izar mamacin a ranar Asabar da misalin karfe 8 na safe.

Bincike ya tabbatar da cewa wanda lamarin ya ritsa da su, gaba daya mazauna yankin na Rigasa ne.

Madugu ya kara da cewa ‘yan bindiga suna yawan kai farmaki kan hanyar da ke kai mutane yankin nasu daga filin jirgin sama.

Sannan ya yi kira da Gwamnatin Jihar Kaduna da ta samo mafita dangane da ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin.