Daily Trust Aminiya - Mahara sun kashe soja, sun sace yara a Zariya

‘Yan Bindiga

Mahara sun kashe soja, sun sace yara a Zariya

’Yan bindiga sun kai hari gidan wani lakcaran Jami’ar Jihar Kaduna, Dokta Ahmed Buba, da ke Zariya, inda suka yi garkuwa da ’ya’yansa shida.

Kazalika, ’yan bindigar sun kashe wani soja mai suna Ebuka Okechukwu, wanda aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti sakamakon rauni da ya samu a harin.

Maharan sun kuma sace Rabi Isya, matar makwabcin Dokta Buba, da ’ya’yanta biyu a harin da suka kai a ranar Litinin.

Sai dai an yi nasarar gano maboyar maharan a ranar Talata.

Wata majiya ta ce ’yan bindigar kusan su 30 dauke da muggan makamai ne suka shiga yankin suna harbi a iska.

“Bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an tsaron hadin gwiwa sun bazama don ceto wadanda aka sace.

“Da suka hangi jami’an tsaron sai suka bude wuta, wanda hakan ya yi sanadin rasa ran soji daya,” a cewar majiyar.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Haruna Shika ya ce an yi nasarar ceto yara shida da ’yan bindigar suka sace a Kasuwar Da’a da ke Karamar Hukumar Zariya.

Da take bayani a kan lamarin a ranar Talata, mataimakiyar kakakin rundunar sojin Kasa ta Najeriya a Zariya, ta ce ba ta da labarin mutuwar sojan.

Kokarinmu na jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige kan lamarin ya ci tura har muka kammala hada wannan rahoton.

Karin Labarai