✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe ’ya’yan manomi sun sace wasu

An baza jami'an tsaro a yankin don gano inda maharan suka shiga.

Mahara ne sun kashe ’ya’yan wani manomi suka kuma yi garkuwa da wasu ’ya’yansa biyu a lokaci guda.

Maharan sun kuma nemi shiga gidan wani makiyayi mai suna Yinka Oludotun, amma ba su samu nasara ba.

  1. Saudiyya ta kashe matashi kan laifin da ya aikata yana karami
  2. Sojoji: Har yanzu akwai aiki babba a gabanku — Buhari

Wata majiya ta ce, “Rashin nasarar shiga gidan Yinka ne ya sa suka shiga gidan Dele suka kashe ’ya’yansa biyu sannan suka sace biyu.”

Manomin mai suna Dele na zaune ne a yankin Ajowa Akoko Karamar Hukumar Akoko ta Yamma a Jihar Ondo.

Majiyarmu ta ce zuwan sojoji ne ya hana maharan shiga gidan makiyayin da suka so su fara shiga tun farko.

Ta ce jami’an tsaro sun yi wa dajin yankin Ajowa Akoko kawanya, suna sintirin gano maboyar maharan.

Kakakin ’yan sandan jihar, Tee-Leo Ikoro, ya ce jami’an tsaro na binciken inda maharan suka shiga.

Ikoro ya ce za su tabbatar an kubutar da yaran cikin koshin lafiya.

“Tabbas, an yin garkuwa da wasu a yankin Ajowa kuma muna kan gudanar da bincike,” inji shi.